
Gwamnatin jihar Katsina ta sallami manyan jami’an kungiyar kwallon kafa ta Katsina United Fc daga aiki sakamakon rashin ci shida da suka yi da kungiyar Ikorodu City Fc a kan MD 31 a gasar da ke gudana.
Wadanda aka sauke daga ayyukansu sune kamar haka:-
1:- Gaddafi Muammar Rudwan,
2:- Abbas Tukur
3:- Abdullahi Umar Leda Danja
4:- Yasir Yahaya da
5:- Abubakar Adidas.
Korar ta fara aiki nan take kuma suna ba da shawara su mika al’amuran kungiyar ga ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa Alh Rabiu Muhammad Rabiu da tawagar wasu ma’aikata biyu wato Saleh Yusuf da Aminu Leno.
Kwamishinan Matasa da Cigaban Wasanni ne ya nada su wanda zai kula da yadda kungiyar Darling ta Katsina United Fc ta jaha har zuwa wani lokaci.
Katsina United Fc
Media Directorate.