
Wata motar bas mai dauke da fasinjoji 20 a kan hanyar Malumfashi zuwa Kafur ta yi hatsarin da ya yi sanadin mutuwar mutane tara tare da jikkata wasu 11.
Aliyu Ma’aji, kwamandan sashen hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Katsina.
Ya alakanta hatsarin da ya afku a garin Malumfashi da wuce gona da iri, wanda ya sa direban ya rasa iko da motar.
Ya ci gaba da cewa, “Hukumar FRSC reshen jihar Katsina ta sanar da jama’a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a garin Malumfashi, dake kan titin Malumfashi zuwa Kafur.
Ya yi sanadiyar mutuwar mutane tara da ke tafiya a cikin wata motar bus ta Hummer dauke da mutane 20, an ceto mutane 11 kuma yanzu haka suna karbar magani a asibiti saboda raunuka daban-daban.
A karshe ya bukaci masu ababen hawa da su yi taka-tsan-tsan a lokacin bukukuwan, tare da gargadin gujewa wuce gona da iri, da tukin ganganci da ka iya janyo asarar rayuka duk da kyawawan hanyoyi.