
Shugaban Kwamitin Sojoji na Majalisar, Alhaji Aminu Balele Kurfi Danarewa ya ji dadin yadda al’ummar Musulmi suka yi amfani da lokacin bukukuwan Sallah wajen rokon Allah Ya kawo mana karshen kalubalen tsaro da ke addabar wasu sassan kasar nan.
Alhaji Aminu Danarewa wanda shi ne dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Dutsinma Kurfi ya yi wannan kiran a sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi.
Dan majalisar ya bayyana bukukuwan Sallah a matsayin lokacin nuna soyayya ga juna da kuma ziyarar abokai da dangi da sauransu.
Ya tunatar da al’ummar mazabarsa da jihar Katsina da ma kasa baki daya cewa gwamnati a kowane mataki ta himmatu wajen ganin kalubalen tsaro ya zama tarihi.
Alhaji Aminu Danarewa ya taya al’ummar musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan tare da addu’ar Allah ya kara shaida.