
Gwamnatin tarayya ta sanar da wani shiri na samar da cibiyoyin canza man gas (CNG) da kuma gidajen mai a manyan makarantun gwamnatin tarayya 20 a fadin Najeriya.
Wannan yunƙurin yana da nufin haɓaka karɓar makamashi mai tsafta da rage farashin sufuri ga ɗalibai da malamai.
A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon fadar shugaban kasar Najeriya, X (tsohon Twitter) a ranar Litinin, shirin yana gudana ne da Asusun Midstream and Downstream Gas Infrastructure Fund (MDGIF) tare da hadin gwiwar Femadec Energy.
Sanarwar ta kara da cewa, “A daidai lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin samar da makamashi mai araha, mai tsafta da kuma dorewa, Asusun Midstream da Downstream Gas Infrastructure Fund (MDGIF), tare da hadin gwiwar Femadec Energy, an saita don kafa cibiyoyin musayar iskar Gas (CNG) da tashoshin mai a fadin manyan makarantun tarayya 20 a duk fadin kasar.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa, kwanan nan Ministan Ilimi, Dakta Morufu Olatunji Alausa, ya gana da mataimakan shugabanni da wakilai daga MDGIF, Femadec Energy, da Presidential Compressed Natural Gas Initiative (PCNGI) don kammala cikakkun bayanan aikin da kuma tabbatar da aiwatar da aiwatar da ayyukan a kan kari yana mai tabbatar da cewa ana sa ran shida daga cikin cibiyoyi za su sami cikkaken cibiyoyi25 na CNG a ranar 2 ga Mayu.