
Karamin Ministan Ayyuka, Muhammad Goronyo, a wata ziyara da ya kai Katsina a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana cewa wasu manyan tituna guda biyar a Katsina na daga cikin hanyoyin da gwamnatin tarayya ta yi tanadin kasafin kudi domin kammalawa.
A cikin bayaninsa, ya ce, “A jihar Katsina kadai, an tsara hanyoyi biyar da za a aiwatar da su sun hada da titin Katsina-Kano, titin Kano-Daura-Kongolom, da titin Kwanar Babangida-Kagara, da kuma titin Kafur-Dabai-Malumfashi da Katsina-Kazaure-Maiadua.
Mataimakin gwamnan jihar Farouk Jobe ne ya tarbe shi a fadar gwamnati a madadin gwamna Dikko Radda a wani bangare na ziyarar fahimtar da ministar kan ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa musamman a yankin Arewa maso yammacin kasar nan.
Ministan ya ci gaba da bayyana cewa, “Ina bin umarnin shugaban kasa na tantance dukkan ayyukan da gwamnatin da ta gabata ta fara a shiyyoyin siyasar kasar nan shida.
“Gwamnatin tarayya ta yi tanadin isassun kasafin kudi domin kammala ayyukan da ake gudanarwa da kuma sabbi da shugaban kasa ya kaddamar.
“A bisa sabon tsarin, yanzu gwamnatocin jihohi za su dauki nauyin biyan diyya ga masu filayen da za a saya don ayyukan tituna.”
Don haka ya bukaci gwamnatin jihar da ta samar da tsaro ga kamfanin gine-gine domin tabbatar da gudanar da ayyukan a kan lokaci.
Shi kuwa mataimakin gwamnan jihar Katsina Faruk Jobe a nasa bangaren ya jaddada kudirin gwamnati na gaggauta kammala aikin hanyar tarayya daga Katsina zuwa Kano.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta nemo hanyar da za ta bi wajen biyan diyya ga masu filayen da aka yi amfani da su wajen aikin hanyar kamar yadda tsarin babbar hanyar tarayya ta tanada.
Jobe ya kuma jaddada bukatar tabbatar da gudanar da aikin kamar yadda aka tsara.
A nasa jawabin, “Gwamnatin Jiha na da sha’awar aikin titin na daya daga cikin muhimman ayyukan da ba wai kawai za su kawo sauyi ga harkokin tattalin arziki a Jihar ba har ma da inganta rayuwa da tsaro a fadin Arewa maso Yamma.
A karshe ya yabawa gwamnatin tarayya kan ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a jihar tare da kaddamar da wasu sabbi tare da yin alkawarin samar da isasshen tsaro daga gwamnatin jihar ga kamfanin gine-gine domin gudanar da aikin.