
Mai shari’a Musa Danladi Abubakar, a lokacin rabon kayan abinci da nade-nade ga yara marayu da marasa galihu 50 da kungiyar JIBWIS ta shirya a masallacin Juma’a na Kandahar Kofar Kaura Katsina, ya bukaci masu hannu da shuni da su yi amfani da dukiyarsu wajen taimakon marayu da marasa galihu a cikin al’umma.