
Gwamnatin jihar Katsina ta jaddada kudirinta na sake fasalin fannin ilimi tare da bayar da tabbacin daukar matakin da ya dace a kwalejin kimiyyar likitanci ta Jami’ar Ummaru Musa yaradua katsina.
Kwamishinan ma’aikatar fasaha da koyar da sana’o’i Alh Isah Muhammad Musa ya bayyana haka a lokacin da yake duba aikin gina dakunan kwanan dalibai da katangar bango a kwalejin da kuma gina Hostels mata a Hassan Usman Katsina Polytechnic.
Alh Isah Musa ya bayyana cewa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Dikko Umar Radda ta ba da fifiko wajen kyautata rayuwar dalibai da malamai, don haka akwai bukatar a samar da yanayi mai kyau na koyo ta hanyar gina dakunan kwanan dalibai na duniya ga daliban jihar.
Kwamishinan wanda ya nuna jin dadinsa kan matakan da aikin ya kai, ya bayyana kwarin gwiwar cewa gwamnatin jihar za ta cika ka’idojin hukumar kula da jami’o’i ta kasa domin daukar matakin da ya dace daga kwalejin kimiyyar likitanci ta jami’ar.
Akan gina sabbin dakunan kwanan dalibai mata na Hassan Usman Katsina Polytechnic, kwamishinan ya bada tabbacin cewa kokarin zai jawo karin dalibai mata da zasu shiga makarantar tare da fatan samun ingantaccen muhalli.
Alh Isah Musa ya ja kunnen daliban da suka amfana da su yi amfani da kayayyakin bisa ga gaskiya domin ci gaban ilimi.
Ya kuma shawarci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da tsaron ginin ga al’umma masu zuwa.