
Wata kotu a Dubai ta yanke wa mai kamfanin Rahmaniya Group and Ultimate Oil & Gas, Abdulrahman Bashar hukuncin daurin shekara daya a gidan yari, bisa samunsa da laifin yin mu’amala da kamfanin CI Energy Company, wani kamfanin mai da iskar gas wanda ya zama karo na biyu cikin kasa da shekaru biyar da za a yanke masa hukuncin dauri.
A shekarar 2020, wata kotu a Birtaniya ta kuma yanke wa Abdulrahman Bashar hukuncin daurin watanni goma a gidan yari.
A cewar takardun kotu, kotun Hadaddiyar Daular Larabawa ta yanke hukuncin daurin da aka yanke a ranar 30 ga watan Janairun 2025 duk da cewa Mista Bashar, mai shekaru 48, ya kasa halartan shari’a duk da an sanar da shi.
Masu gabatar da kara a Hadaddiyar Daular Larabawa sun tuhume shi da laifin bayar da cak guda bakwai da kudinsu ya kai Dirhami miliyan 126.45, wadanda aka zana a asusun bankin Musulunci na Emirates da rashin daidaito a cikin sa hannun sa.
Ana zarginsa da bayar da cak din ta hanyar “sa hannun da gangan tare da tsara su ta hanyar da za ta hana karbar kudadensu,” saboda haka yana neman a hukunta Mista Bashar a karkashin wasu dokoki.
Dogaro da shaidun da aka gabatar wa kotun, ciki har da kalaman Jamal Awad Nasser Hussein (wakilin CI Energy), kwafin cak da bayanan asusun, ya lura cewa an mayar da cek din ne ba tare da biya ba a lokacin da aka gabatar da su a bankin Islama na Emirates saboda rashin daidaito a sa hannun Mista Bashar.
Kotun, a yayin ci gaba da zaman da mai shari’a Hussein Hamdi ya jagoranta ta ce, “An tabbatar da cewa laifin bayar da cak yana samuwa ne kawai ta hanyar bai wa wanda ya ci gajiyar cakin, sanin cewa babu wani ma’auni na cirewa.
“Kotu ta ga daga binciken takardun cewa abin da ya faru a cikin iyakokin abin da ta zayyana ta hanyar da aka ambata ya isa ya kafa wanda ake tuhuma don yanke masa hukunci.”