Rundunar ‘yan sandan jihar Kataina ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a babban asibitin Kankara.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Abubakar Aliyu ya tabbatar da hakan ta wata sanarwa a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce “A ranar 14 ga watan Janairu, 2025, da misalin karfe 10:20 na rana, wasu da ake zargin ‘yan bindiga dauke da muggan makamai, kamar bindigar AK-47, suna harbi lokaci-lokaci, sun kai hari babban asibitin Kankara.
“Bayan samun rahoton, sai da DPO na ofishin ‘yan sanda reshen Kankara ya yi gaggawar tashi tare da mayar da martani inda aka yi artabu da bindiga, wanda ya yi sanadiyyar dakile harin.
“Abin takaicin, an harbi mutum biyu tare da raunata a yayin harin, Dakta Murtala Saleh, mai shekaru 30, mai shekaru 30, likita a asibiti, an harbe shi tare da raunata a cinyar dama, yayin da wani mai suna Kamala Suleiman mai shekaru 20 da haihuwa. Wadanda suka jikkata a gwiwarsu a halin yanzu suna samun kulawar lafiya kuma suna cikin kwanciyar hankali.
“Bugu da kari, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane uku, ana kokarin ganin an ceto wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da samun matsala ba tare da damke wadanda suka aikata wannan danyen aikin.
“Kwamishanan ‘yan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, psc+, yayin da yake yin Allah wadai da wannan hari na rashin imani da aka kaiwa ma’aikatan lafiya da cibiyoyin, ya bayar da umarnin tura karin kadarorin aiki zuwa wurin domin inganta tsaro da kuma zafafa farautar maharan.
“Za a sanar da ƙarin ci gaba a kan lokaci yayin da bincike ya ci gaba.”