SANARWA: GWAMNATIN KATSINA
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya jagoranci bikin bude sabon masallacin Juma’a a garin Sandamu dake karamar hukumar Sandamu a jihar Katsina.
Masallacin mai suna Masjid Sardauna, an gina shi ne bisa karimcin mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mustapha Mohammed Bala, wanda a yanzu haka yake rike da mukamin AIG na shiyya ta 6, Calabar.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin, Gwamna Radda ya yabawa AIG Bala bisa gina ginin addini a yankin.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da suka amfana da su da su yi amfani da wannan damar ta hanyar da ta dace, inda ya shawarce su da su kafa kwamitin da zai tabbatar da kula da Masallacin.
Taron na musamman ya samu halartar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar Faruq, wanda ya nada babban limamin masallacin Sardauna, Imam Yusuf Muhammad. Ya kuma bukaci malaman addini da su kara himma wajen wayar da kan mabiyansu a kan koyarwa da darussa na Musulunci.
Imam Muhammad ya kara limanci raka’a biyu a masallacin. A cikin hudubarsa ta Juma’a, ya jaddada muhimmancin saka hannun jari a harkokin addinin Musulunci domin neman lada a wurin Allah Madaukakin Sarki.
Shi ma Sheikh Abdullahi Kaduna, ya bukaci ‘yan uwa musulmi da su kara kaimi wajen yi wa shugabanni addu’a a kasar nan.
Gwamnan ya samu rakiyar ‘yan majalisar zartarwa ta jiha da manyan jami’an gwamnati a kasar nan.
Ibrahim Kaula Muhammad
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Katsina
10 Janairu, 2025