Majalisar dokokin jihar Jigawa ta amince da kudurin kasafin kudi na shekarar 2025 na sama da naira biliyan 698 na ayyukan gwamnatin jihar da kuma naira biliyan 184 na ayyukan kananan hukumomi 27.
Hakan ya biyo bayan gabatarwa da kuma amincewa da rahoton zaunannen kwamitin kasafin kudi na majalisar.
Da yake gabatar da rahotan shugaban kwamatin wanda shi ne mamba mai wakiltar mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim ya bayyana cewa dukkanin kwamitocin majalisar sun tantance tanade-tanaden kasafin kowace ma’aikatar da hukumar domin yiyuwar gyara ko kari a cikin kasafin kudin. .
A cewarsa, kwamitocin sun kuma yi da masu ruwa da tsaki daban-daban da suka hada da kungiyoyin farar hula tare da gudanar da aikin tantancewa a kokarin da ake na isa ga wani cikakken takardar kasafin kudi domin gabatar da shi ga zaman majalisar.
Bayan amincewar baki daya ta hanyar kada kuri’a, kakakin majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya sanar da amincewa da kudurin kasafin kudin shekarar 2025 ya zama doka.
Daga Aminu Musa Bukar