Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC) ta yi ikirarin cewa kashi 76 cikin 100 na mutanen da suka fuskanci bukatu na cin hanci a yankin Arewa maso Yamma sun ki amincewa da karbar mafi girman kima a tsakanin shiyyoyin siyasar Najeriya a matsayin wata alama da ke nuna adawa da cin hanci a yankin, yayin da 70 kashi 100 na ’yan Najeriya da aka tunkare su domin karbar cin hanci a shekarar 2023 sun ki bin doka a fadin kasar.
Shugaban Hukumar Musa Aliyu ne ya bayyana haka a ranar Litinin din da ta gabata yayin wani taro da ICPC da manyan lauyoyin jihar a shiyyar Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kano inda aka mai da hankali kan inganta kwazon hukumar na dakile cin hanci da rashawa.
Aliyu ya bayyana sakamakon da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da muggan kwayoyi (UNODC) suka fitar a shekarar 2023 na cin hanci da rashawa a Najeriya: Rahoton Patterns and Trends, inda ya yi nuni da yawaitar cin hanci da rashawa a yankin Arewa maso Yamma da fadin kasar nan.
Ya ce: “An fi samun cin hanci a cikin ma’aikatun jama’a, jami’an tsaro, da ayyukan gudanarwa.
“Kodayake, duk da wadannan kalubale, labari mai dadi shine kashi 70 cikin 100 na ‘yan Najeriya sun nemi cin hanci a shekarar 2023 sun ki amincewa a kalla sau daya.
“A Arewa maso Yamma, kashi 76 cikin 100 na mutanen da suka fuskanci buƙatun cin hanci sun bijirewa – mafi girman ƙima a tsakanin shiyyoyin siyasar Najeriya, wanda ke nuna adawa da cin hanci a yankin.”
Da yake jaddada nauyin daya rataya a wuyan gwamnatocin Jihohi da na tarayya wajen yaki da cin hanci da rashawa, Aliyu ya ce, hadin kai ya zama dole wajen gina tsarin gaskiya da rikon amana.
Ya bukaci al’ummar yankin arewa maso yamma da su yi watsi da bukatar cin hanci da rashawa, yana mai jaddada kudirin hukumar ICPC na yin amfani da ikonta wajen yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata.
Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa a yaki da cin hanci da rashawa, inda ya yi nuni da ginshikin biyar na dabarun yaki da cin hanci da rashawa na Najeriya (NACS II), wanda ke mayar da hankali kan hadin gwiwa.