Gwamnan jihar Kebbi, Kwamared Nasiru Idris, ya bayar da umarnin a kamo wadanda ke da hannu wajen kai harin ramuwar gayya ga Fulani bayan harin Mera da ‘yan ta’addan suka kai.
Gwamnan wanda ya ba da umarnin a ziyarar jaje da ya kai garin Mera da ke karamar hukumar Augie a jihar, ya yi Allah wadai da harin ramuwar gayya da aka kashe Fulani shida a yankin.
Gwamnan ya bayyana cewa, ba daidai ba ne daidaikun mutane su dauki doka a hannunsu kuma gwamnatinsa ba za ta amince da ayyukan adalci na daji a jihar ba.
A cewarsa duk wani tuhuma da ake yi a kai rahoto ga hukumomin tsaro da suka dace domin daukar matakin gaggawa maimakon daukar doka a hannunsu.
Gwamna Idris, ya yi gargadin cewa, gwamnatinsa ba ta da juriya ga ayyukan ‘yan fashi, kuma za ta ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya don ci gaba da kai farmakin tare da magance tsangwama ga duk wani mai ba da labari ga ‘yan bindiga a jihar.
An kai harin ne kan Fulanin da ake zargin suna da hannu a harin Mera da kungiyar ta’addancin ta kashe mutane 17.