Wata babbar mota da ke dauke da bututun iskar gas ta fashe da safiyar Juma’a a wata tashar mai da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda ta lalata motoci shida a cikin lamarin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.
Ya bayyana cewa: “A yau, 15 ga Nuwamba, 2024, da misalin karfe 8.45 na safe, jami’an ‘yan sanda da ke hedikwatar ‘yan sanda na Jibia suka ji karar fashewar wani abu mai karfi.
“Da take mayar da martani, DPO ya jagoranci jami’an tare da hadin gwiwar sojoji zuwa wurin da lamarin ya faru.
“Da isar jami’an ‘yan sandan ne suka tarar da wata mota makare da injinan iskar gas ta kone kurmus a gidan mai na Tamal da ke kan titin Kagadama- Magama Jibia a karamar hukumar Jibia.
“Tawagar hadin gwiwa ta gaggauta daukar matakan kariya domin kare rayuka da rage asarar dukiyoyi, inda suka yi nasarar kashe gobarar.
“Motoci shida ne gobarar ta shafa sosai, amma aka yi sa’a, ba a rasa rayuka ba.
Aliyu ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Musa jad ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike “don gano musabbabin fashewar.
Ya ce za a sanar da ƙarin ci gaba yayin da bincike ya ci gaba.