Ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar Katsina ta tallafa wa matasa biyar masu bukata ta musamman da wasu shida da tallafin kudi domin inganta sana’o’insu.
Babban sakataren ma’aikatar Muhammad Rabi’u Muhammad ya mika tallafin kudi ga matasan da suka ci gajiyar tallafin a madadin kwamishina Aliyu Lawal Zakari.
Da yake gabatar da tallafin kudi, sakatare na dindindin Muhammad Rabiu Muhammad ya bayyana godiyarsa ga kokarin gwamnan jihar Malam Dikko Umar Radda na bayar da tallafin kudin don tallafawa rayuwar matasa domin su tsaya da kafafunsu.
Muhammad Rabiu Muhammad ya jaddada kudirin ma’aikatar na ci gaba da baiwa matasa damar dogaro da kai inda ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kudaden da suka karba ta hanyar da ta dace.
Tun da farko Daraktan Matasa na Ma’aikatar Sani Yahaya ya ce an taimaka wa matasa goma sha daya da suka amfana bayan sun halarci horon koyon sana’o’i daban-daban a Kano da Filato.
A madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Maryam Ahmad da Nasiru Yan’siliyu, sun nuna jin dadinsu ga gwamna Malam Dikko Umar Radda da ya bada gudunmawar kudin tare da yin alkawarin yin amfani da kudaden da aka basu yadda ya kamata.