Tafiyar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zuwa kasar Samoa domin wakiltar Najeriya a taron kungiyar kasashen renon Ingila ta shekarar 2024 ta soke sakamakon wani abu da ya afkawa jirginsa a lokacin da ya tsaya a filin jirgin sama na JFK dake birnin New York inda ya yi barna a gaban gilashin jirgin.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru ya bayyana a daren ranar Alhamis.
A cewarsa, “Shugaba Tinubu, wanda ya dauki matakin gaggawa, ya amince da tawagar ministoci da za su wakilci Najeriya a taron da za a yi a babban birnin Samoa na Apia yayin da aka fara gyaran jirgin.
“Tawagar wacce a yanzu za ta wakilci Najeriya a taron Commonwealth na 2024 da za a yi a Samoa, Ministan Muhalli Balarabe Abbas Lawal ne ke jagorantar ta.
“An fara taron ne a tsibirin Pacific a ranar 21 ga watan Oktoba. Za a kammala shi a ranar 26 ga Oktoba.
Ta kara da cewa, mataimakin shugaban kasa Shettima da ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar sun bar birnin New York zuwa Najeriya.