Shugaba Bola Tinubu ya sanar da tafiyar ministoci 10 zuwa ma’aikatu daban-daban a cikin wata sanarwar manema labarai da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Larabar da ta gabata, sabon nadin ya zo ne a daidai lokacin da aka kori ministoci biyar tare da yin garambawul ga majalisar ministocinsa.
Sunayen ministocin da aka kora dai Barr. Uju-Ken Ohanenye, ministar harkokin mata; Lola Ade-John, ministar yawon bude ido; Farfesa Tahir Mamman SAN OON, Ministan Ilimi; Abdullahi Muhammad Gwarzo, karamin ministan gidaje da raya birane; da Dr. Jamila Bio Ibrahim, ministar ci gaban matasa.
Sabbin ministocin da aka nada sune: Hon Dr. Yusuf Tanko Sununu, Dr. Morufu Olatunji Alausa, Barr. Bello Muhammad Goronyo da Hon. Abubakar Eshiokpekha Momo.
Sauran sun hada da Uba Maigari Ahmadu, Dr. Doris Uzoka-Anite, Sen. John Owan Enoh, Imaan Sulaiman-Ibrahim, Ayodele Olawande, da Dr. Salako Iziaq Adekunle Adeboye.