A ranar Larabar da ta gabata ne fadar shugaban kasar ta sanar da cewa an soke ma’aikatar Neja Delta da ma’aikatar wasanni domin sabuwar ma’aikatar raya yankin da za ta rika kula da dukkanin hukumomin raya yankin sannan kuma hukumar wasanni ta kasa za ta karbi ragamar ma’aikatar wasanni.
Bayo Onanuga ya bayyana cewa, FEC ta yanke shawarar cewa a yanzu za a samu ma’aikatar ci gaban yankin da za ta rika kula da dukkan kwamitocin raya yankin da suka hada da Hukumar Raya Neja-Delta, Hukumar Cigaban Arewa Maso Yamma, Hukumar Raya Kudu maso Yamma, Hukumar Raya Arewa maso Gabas.
Haka kuma hukumar wasanni ta kasa za ta karbi ragamar ma’aikatar wasanni.
Ya rubuta cewa, “Shugaba Tinubu da majalisar zartaswa ta tarayya sun yi watsi da ma’aikatar Neja-Delta da ma’aikatar raya wasanni, yanzu za a samu ma’aikatar ci gaban yankin da za ta rika kula da dukkanin hukumomin raya yankin, kamar hukumar raya yankin Neja-Delta, hukumar raya yankin Arewa maso Yamma. Hukumar raya Kudu Maso Yamma, Hukumar Cigaban Arewa maso Gabas.
“Hukumar wasanni ta kasa za ta karbi ragamar ma’aikatar wasanni, FEC ta kuma amince da hadewar ma’aikatar yawon bude ido da ma’aikatar al’adu da tattalin arziki, an yanke shawarar ne a yau a taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja. .”