Yayin da hukumar rigakafin cutar Polio ke shiga rana ta karshe a karamar hukumar Daura da Sandamu, aikin ya samu nasara a yankunan biyu.
A Daura, kodinetan hukumar lafiya matakin farko, Mujitaba Bala Zango, ya ce kimanin yara dubu saba’in da tara da dari daya da goma sha biyu ne aka yiwa riga-kafi a unguwannin goma sha daya.
Mujitaba Bala Zango wanda ya samu wakilcin Malamin Lafiya, Lawal Tijjani Shargalle ya ce ma’aikatar PHC ta samu allurar rigakafi dubu tamanin da uku da dari daya. Ya ce kimanin mutane saba’in da uku gida-gida da tawagar musamman ashirin da tara ne suka halarci atisayen.
A Sandamu, kimanin yara dubu hamsin da hudu da dari bakwai da saba’in ne aka yiwa rigakafi a fadin yankin.
Kodinetan PHC Lawal Aminu ya bayyana haka ta bakin Malamin Fasaha na Jiha Abdulraman Yahya.
Lawal Aminu ya ce sama da kashi 80 cikin 100 an samu nasara tare da gagarumin kokarin shugabannin gargajiya da jami’an lafiya da sauran masu ruwa da tsaki.