Talata, 1 ga Oktoba, 2024 ta zama ranar hutu domin murnar cikar Najeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai da gwamnatin Najeriya ta yi.
Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a madadin gwamnatin Najeriya a wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar, Dakta Magdalene Ajani ya fitar.
A nasa jawabin, Tunji-Ojo ya taya ‘yan Najeriya na gida da waje murnar zagayowar wannan rana, ya kuma yabawa masu hakuri da kuma jajircewa a Najeriya maza da mata, inda ya bayyana cewa sadaukarwar da suka yi ba za ta kasance a banza ba.
Ya sake nanata bukatar ‘yan Najeriya su yi tunani a kan “aikin da jaruman mu suka yi a baya da kuma karfafa gwiwar ayyukan da ke gaba, sanin cewa Nijeriya mai burin mu za ta iya ginawa ne kawai idan muka hada kai.”
Tunji-Ojo da yake yiwa ‘yan Najeriya fatan murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kai, ya bukaci ‘yan kasar da su ci gaba da jajircewa wajen gina kasa.