Jami’an tsaro sun yi nasarar ceto mata uku da yara uku da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar 26 ga Satumba, 2024, a karamar hukumar Jibia, jihar Katsina.
Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar Dr Nasir Muazu ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutanen ne a lokacin da suke aikin girbin masara a wata gona da ke kusa da kauyen Gurbi Magariya.
A cewarsa, ‘yan banga na yankin da suke aiki tare da Community Watch Corps, Sojoji, ‘Yan Sanda, Civil Defence, da DSS, a cikin gaggawar mayar da martani, sun bi ‘yan fashin tare da kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.
Ya ce gwamnatin jihar ta yaba da kokarin hukumomin tsaro da ’yan banga wajen ganin an dawo da mutanen da aka sace lafiya.