Gwamnatin tarayya ta yi hasashen za a samu ruwan sama na kwanaki biyar wanda zai iya haifar da ambaliya a jihohi 21 da kuma wurare 123. Haka kuma an lissafta jahohi bakwai wadanda da alama hakan zai iya shafan su sosai.
Jihohin da wuraren su ne Jihar Adamawa (Mubi, Shelleng, Demsa, Numan, Song, Wuro Bokki, Natubi, Mayo Belwa, Jimeta, Gbajili, Ganye, Farkumo, Abba Kumbo), Jihar Benue (Udoma, Ugbokpo, Ugbokolo, Ukpiam, Otobi, Otukpo, Mbapa, Makurdi, Gbajimba, Gogo, Abinsi), Jihar Bauchi (Azare, Jama’are, Itas, Misau, Tafawa-Balewa), Jihar Kogi (Ugwalawo, Idah, Ibaji, Wara, Omala, Bassa, Ajaokuta), Jihar Borno (Biu, Maiduguri, Briyel), Jihar Nasarawa (Ado, Mararaba, Udeni, Rukubi, Ajima, Odogbo), Jihar Gombe (Nafada, Gombe, Bajoga), Jihar Kwara (Kosubosu, Kaiama), Jihar Jigawa (Dutse, Gumel) , Ringim), Jihar Oyo (Kishi).
Sauran jihohin sun hada da Jihar Kaduna (Kachia, Zaria, Kauru, Jaji), Jihar Edo (Udochi, Agenebode), Jihar Kano (Sumaila, Kunchi, Karaye, Gwarzo, Bebeji, Tudun wada), Jihar Katsina (Bakori, Bindawa, Funtua, Jibia, Kaita, Katsina, Daura), Jihar Kebbi (Ribah, Argungu, Gwandu, Yelwa, Saminaka, Jega, Bunza), Jihar Plateau (Mangu), Jihar Niger (Ibi, New Bussa, Mashegu, Kontagora, Lavun, Rijau, Magama, Lapai, Katcha, Bida).
Jihar Sokoto ( Isa, Makira, Gagawa, Shagari, Silame, Goronyo), Jihar Taraba (Ngaruwa, Serti, Yorro, Natubi, Mutum biyu, Kwata kanawa, Lau, Kambari, Jalingo, Gun-gun Bodel, Gassol, Garkowa, Bandawa, Beli, Bolleri, Mayo Renewo, Duchi), Jihar Yobe (Geidam, Potiskum, Dapchi, Damaturu), da Jihar Zamfara (Bukkuyum, Gummi, Kaura Namoda, Shinkafi, Maradun).
Ayi Share. Yana iya kiyaye wani lafiya.