Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina ta sanar da fara yakin neman zabe a ranar Asabar 14 ga watan nan na dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Shehu Sarki Idris ya rabawa manema labarai.
A cewar sanarwar, hakan ya yi daidai da jadawalin da aka amince da shi na gudanar da zabukan kananan hukumomi, wanda zai gudana a ranar 15 ga watan Fabrairun 2025.
Sanarwar ta nuna cewa ana gudanar da ayyukan hukumar bisa ka’idojin da aka amince da su da kuma jadawalin zaben da za a fitar ga jama’a a watan Fabrairun 2024.
Sanarwar ta kuma tunatar da duk jam’iyyun siyasar da ke son shiga zaben da kuma ‘yan takararsu kan bukatar bin ka’idojin da aka gindaya domin rashin bin ka’idojin na iya haifar da soke takarar.