Tinubu ya taya Radda murnar cika shekaru 55

Da fatan za a raba

Shugaba Bola Tinubu ya taya gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda murnar cika shekaru 55 a ranar Talata.

Shugaban ya ce gwamnan ya yi rayuwa mai tasiri ta bangarori da dama na sana’arsa ta sirri da ta gwamnati, har ya kai ga zaben sa a matsayin gwamna a 2023.

Shugaba Tinubu ya ce kamata ya yi rayuwar Gwamna Radda ta zaburar da matasan Najeriya masu sha’awar yin sana’o’in hannu.

Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa Tinubu shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ta kara da cewa shugaban kasar ya yi addu’ar Allah ya kara wa Gwamna Radda samun nasarori tare da bukace shi da ya sadaukar da kansa wajen yi wa al’ummarsa hidima da kuma Nijeriya.

  • Labarai masu alaka

    An Bukaci Iyaye Mata Su Bada Muhimmanci Ga Duba Lafiyarsu A Kullum Domin Hana Yaɗuwar Cutar HIV Daga Uwa Zuwa Jariri

    Da fatan za a raba

    An ƙarfafa iyaye mata su riƙa ziyartar cibiyoyin lafiya mafi kusa akai-akai don sa ido kan yanayin lafiyarsu, musamman a lokacin daukar ciki.

    Kara karantawa

    Bikin Kasuwanci: Matasa Suna Shirya Makomar Yau

    Da fatan za a raba

    An yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu na Jihar Katsina da su gano ra’ayoyi masu kyau, su ba da jagoranci ga matasa ‘yan kasuwa, da kuma zuba jari a harkokin kasuwanci da matasa ke jagoranta.

    Kara karantawa

    0 0 kuri'u
    Ƙimar Labari
    Subscribe
    Sanar da
    guest

    0 Sharhi
    Mafi tsufa
    Sabuwa Mafi Yawan Zabe
    Jawabin cikin layi
    Duba duk sharhi

    Labarai daga Jihohi

    Gwamna Abdulrazaq ya yi Allah wadai da harin Eruku,

    Gwamna Abdulrazaq ya yi Allah wadai da harin Eruku,

    YAN QARSHE SHIDA SUKA FITO A GASAR KW-IRS TAX KLUBU 2025

    YAN QARSHE SHIDA SUKA FITO A GASAR KW-IRS TAX KLUBU 2025
    0
    Bayyana tunanin ku kuma sami bayanai kyautax
    ()
    x