Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya tarbi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a jihar domin yin ta’aziyyar rasuwar Hajiya Dada Musa Yar’adua, mahaifiyar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua.
Gwamna Radda tare da rakiyar Murtala Shehu Yar’adua, jikan marigayin kuma tsohon karamin ministan tsaro, da kuma Inuwa Baba, tsohon babban jami’in hulda da jama’a na shugaba Obasanjo ne suka tarbi babban bako a filin jirgin.
Tawagar dai ba tare da bata lokaci ba ta wuce gidan Iyalan ‘Yar’aduwa inda Sanata Abdulaziz Musa Yar’adua mai wakiltar shiyyar Katsina kuma hamshakin dan kasuwa Dahiru Barau Mangal ya tarbe shi.
A yayin ziyarar tasa, Cif Obasanjo ya yi matukar tunawa da Hajiya Dada ‘Yar’aduwa a matsayin uwa mai kulawa, inda ya yaba da karimcinta da kyautatawa tare da yi mata addu’a ga Allah ya gafarta mata, ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta mata kurakuranta.
Gwamna Radda ya bayyana godiyarsa ga tsohon shugaban kasa Obasanjo bisa ziyarar da ya kai masa.