Jami’an tsaro na farin kaya (DSS) a jihar Katsina sun gano tare da kwato buhunan shinkafa sama da 1000 daga cikin manyan motoci 20 da gwamnatin Najeriya ta baiwa jihar.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ta ruwaito, an gano shinkafar da aka kwato ana zargin wasu jami’an gwamnatin jihar Katsina ne suka karkatar da su.
Gwamnatin Najeriya ta bayar da tallafin shinkafar ne domin rage wahalhalun da tattalin arzikin kasar ke fuskanta a halin yanzu.
NAN ta ruwaito cewa bincike ya nuna cewa an ajiye buhunan shinkafar mai nauyin kilogiram 25 a babbar kasuwar Katsina, biyo bayan wani rahoto da hukumar DSS ta samu a daren Laraba.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Shehu Usman, ya bayyana cewa wani ba dan kasuwa ne ya shigo da shinkafar ba, inda ya jaddada bukatar ‘yan kasuwa su yi taka-tsan-tsan wajen karbar irin wadannan kayayyaki domin adanawa.
A yayin da yake mayar da martani kan zargin, Mista Aliyu Abdullahi, babban sakatare mai zaman kansa na gwamna Dikko Radda, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kebe shinkafar ga ministan gidaje da raya birane Ahmed Dangiwa.
Ya kuma bayyana cewa ministan ya umurci mai bawa gwamna shawara na musamman kan samar da ababen more rayuwa Alhaji Nasiru Lawal da ya ajiye shinkafar, inda ya yanke shawarar ajiye ta a kasuwa domin adanawa. Shinkafar da aka ware ta kai buhu 1,200 sabanin shekarar 2000 da wasu kafafen yada labarai suka ruwaito.