Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 27 a wani sabon hari da aka kai kan wasu al’ummomi a kananan hukumomin Dutsinma da Safana na jihar Katsina. ‘Yan ta’addan sun kaddamar da hare-hare a kan al’ummomin a ranar Talata yayin da wasu ‘yan bindiga suka mamaye kauyukan Dogon Ruwa, ‘Yar Kuka, Rimi, Lezumawa da sauran kauyuka a ranar Alhamis.
Hare-haren sun tilastawa mazauna garin tserewa tare da neman mafaka a garin Dutsinma da kauyen Turare. An bayyana cewa wasu daga cikin wadanda suka mutun sun hada da mazauna Tashar Kawai Mai Zurfi, Sabon Gari Unguwar Banza, Dogon Ruwa, Sanawar Kurecen Dutsi, Unguwar Bera, Kuricin Kulawa, Larabar Tashar Mangoro, Sabaru, Ashata, Unguwar Ido, Kanbiri, Kunamawar Mai Awaki. a Kunamawar ‘Yargandu.
An tabbatar da mutuwar mutane 27 daga wadannan hare-haren amma babu wani jami’in tsaro a cikin wadanda suka mutu, kamar yadda rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar.
A halin da ake ciki, ‘yan sanda sun kara tura jami’ai zuwa yankunan da lamarin ya shafa domin kare jama’a.