Daraktan Sadarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, Ademola Olajire a ranar Talata ya tabbatar da cewa ‘yan wasan Super Eagles da suka makale a Legas da Abuja sun isa Uyo babban birnin Akwa Ibom.
A cewarsa wasu daga cikin ‘yan wasan Super Eagles an ce suna da kalubale wajen shiga sauran ‘yan wasan a sansanoni, sakamakon yajin aikin NLC/TUC.
Ya ce kungiyoyin da ke yajin aikin sun rufe filayen tashi da saukar jiragen sama na kasar ne a ranar Litinin din da ta gabata, inda suka hana wasu ‘yan wasan Super Eagles, wadanda ya kamata su rika jigilar jirage zuwa Uyo daga Legas da Abuja tashi.
NFF a cikin wata sanarwa, ta ce “jimillan ‘yan wasa 15 sun yi atisaye a safiyar ranar Litinin a Uyo”.
Kociyan kungiyar Finidi George ya bukaci ‘yan wasan da cewa maki ukun da ake da su a karawar ranar Juma’a su kare ne a wasan Najeriya.
Sanarwar ta kuma ce ‘yan wasan baya Semi Ajayi, Bright Osayi-Samuel da Calvin Bassey, dan wasan tsakiya Frank Onyeka da Paul Onuachu sun riga sun isa kasar.
Olajire, ya tabbatar da cewa masu tsaron baya Semi Ajayi, Bright Osayi-Samuel da Calvin Bassey, tare da dan wasan tsakiya Frank Onyeka da Paul Onuachu, sun sauka a filin jirgin sama na Victor Attah.
Olajire ya ce sun sauka ne a Uyo, a cikin wani jirgin sama mai zaman kansa da hukumar NFF ta shirya, kuma an kai su Ibom Hotel da Golf Resort, domin ganawa da abokan wasansu don cin abincin rana.