Kungiyar Kwadago ta dakatar da yajin aikin na kwanaki biyar a fadin kasar domin ba da damar ganawa da kwamitin bangarori uku kan sabon mafi karancin albashi na kasa.
Wata majiya mai alaka da shugabannin kungiyar ta Labour ta bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata.
Shugabannin Kwadago sun yi nasarar ganawa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, George Akume, da sauran jami’an gwamnati a ranar Litinin din da ta gabata, inda suka cimma matsaya kan cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar ganin an fara biyan mafi karancin albashi fiye da N60,000.
Haka kuma sun kuduri aniyar cewa kwamitin uku zai gana a kowace rana tsawon mako guda da nufin isa ga mafi karancin albashi na kasa.
Tare da wannan ci gaban, ana sa ran kowane ofisoshi na gwamnati da masu zaman kansu za su sake buɗewa kuma su yi aiki kamar yadda aka saba.