Uwargidan gwamnan jihar Katsina, Hajiya Zulaihatu Dikko Radda ta jaddada kudirinta na kare hakkin yara da kuma saka jari a rayuwarsu ta gaba.
Uwargidan Gwamnan ta bayar da wannan tabbacin ne a yayin bikin ranar yara ta wannan shekara ta 2024 mai taken ‘sa hannun jari ga ‘ya’yanmu na nufin saka hannun jari a nan gaba’ wanda aka gudanar a dakin liyafa na gidan gwamnati Katsina.
Ta ce babban makasudin bikin na bana shi ne a jaddada mahimmancin saka hannun jari a fannin walwala, ilimi da ci gaban yara baki daya.
Hajiya Zulaihatu Dikko Radda, ta yi kira ga iyaye, masu kulawa da shugabannin al’umma da su sanya hannun jari a kan ‘ya’yanmu don ganin sun samu ingantaccen ilimi, kula da lafiya da muhalli mai kyau.
Tun da farko a nata jawabin shugabar majalisar yara ta jihar Katsina Fadila Sani, ta yaba da kokarin iyaye da Malamai da gwamnati na cusa tarbiyya a cikin su ta yadda za su taso su zama ‘yan kasa na gari.
A yayin taron wasu yara daga makarantu daban-daban sun samu lambar yabo daga uwargidan shugaban kasa saboda kwazon da suka nuna.
Sun hada da Usman Tasiu wanda ya zo matsayi na daya a makarantar firamare ta Garba Kaita ya karbi cek naira dubu 100, Shahid Aliyu na daya daga Gobarau Academy Katsina ya karbi naira dubu 100, Genius Adams daga St. Martins na biyu na sama naira dubu 50, Khadijah. Mustapha na Talented stars Daura na biyu kuma ya samu naira dubu hamsin.
Sauran sun hada da Ovie Godwin daga Unique Learning na 3 na sama ya samu Naira dubu 25 da Chimdahu Jason Naira dubu 25 kuma daga Unique Learning Katsina.